8 Oktoba 2021 - 10:26
​Jami’ar Al-Azhar Za Ta Hada Kai Da Vatican Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya

Shugaban jami’ar al-Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmed Attayyib ya gana da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella a fadarsa da ke birnin Roma a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Egypt Today ta nakalto Ahmed Attayyib a ganawarsa da shugaban ya na fadar cewa Jami’arsa a shirye take ta hada kai da sauran manya-manyan shuwagabannin addinai a duniya, musamman mazhabar catholica don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a bangaren addini a kasashen duniya.

Kafin haka dai shugaban Jami’ar ya gana da paparoma Francis a Vatican inda bangarorin biyu suka cimma matsaya na aiki tare don kawo karshen wuce gona da irin a fagen addini da kuma bunkasa fahintar juna tsakanin mabiya addinai, musamman musulmi da kirista a duniya.

Daga karshe Sheikh Ahmed Attayyib ya bayyana cewa Jami’an Al-azhar ta na da dalibai kimani 30,000 wadanda suka fito daga kasashen duniya fiye da 100.

342/